Nigeria: An sake bude dafon mai a Kano

NNPC na ci gaba da binciken adadin mai da iskar gas da ke karkashin kasa a arewacin Najeriya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption NNPC na ci gaba da binciken adadin mai da iskar gas da ke karkashin kasa a arewacin Najeriya

A Najeriya, Babban kamfanin mai na kasar NNPC ya sake bude dafon mai da ke birnin Kano bayan ya shafe fiye da shekara goma yana rufe.

Kamfanin ya bude dafon ne bayan ya gyara wasu bututan da suka tashi daga Kaduna zuwa Kano wadanda wasu miyagu suka lalata.

Rufe dafon dai ya jefa al`umomin da ke yankin cikin kunci, kasancewar shi ne ya ke samar da albarkatun mai ga jihohi biyar ga kuma dimbin jama`ar da ke samun abin yi a wurin.

Shugaban kamfanin NNPC Engineer Mai Kanti Baru ya shaida wa BBC cewa an kashe sama da Naira biliyan daya da miliyan dari shida wajen gyara butun man kuma ana kashe sama da Naira miliyan dari biyar a kowace shekara wajen kula da bututun man.

A kwanakin baya ne dai kamfanin NNPC ya ce ya sake komawa yankin Chadi don ci gaba da bincike da nufin gano ainihin adadin mai da iskar gas din da ke karkashin kasa a arewacin kasar.

Engineer Maikanti, ya ce NNPC zai yi amfani da wasu manyan na`urori wajen yin binciken kuma idan har abun da aka samu ya kai wani mizani, to kamfanin zai dukufa wajen hakar man.

Tun a shekarun 1970 ne wasu masana da kuma kamfanin NNPC suka yi hasashen cewa za a iya samun mai a yankin, kuma tun daga wancan lokacin aka yi yunkuri daban-daban don binciken man amma ana dakatarwa saboda wasu dalilai, ciki har da zargin cewa akwai siyasa a cikin lamarin.