Amurka ta kulla yarjejeniyar makamai da Saudiya

US President Donald J. Trump with Saudi Arabia"s King Salman bin Abdulaziz Al Saud Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Shugaban Amurka Donald Trump da Sarki Salman na Saudiya

Shugaban Amurka Donald Trump ya sanya hannu a wasu yarjejeniyoyi da Sarki Salman na Saudiyya, da kudinsu ya haura dala biliyan dari uku da hamsin.

A ziyarar shi ta farko zuwa wata kasar waje, Mista Trump ya sanya hannu a yarjejeniyar makamai ta kudi dala biliyan dari da goma sa Saudiya.

Sakataren harkokin wajen Amurka, Rex Tillerson ya ce manufar yarjejeniyar ita ce a taimakawa Saudiya ta shawo kan abin da ya kira karfin fada aji na Iran.

Saudiya ta shirya kasaitacciyar tarba ta alfarma ga shugaba Donald Trump, inda har Sarki Salman ya ba shi lambar yabo mafi girma.

Ministan harkokin wajen Saudiya ya ce ziyarar, masomi ne na sauya yadda al'amura suke tsakanin Amurka da kasashen Larabawa Musulmai.