Arsenal ta rasa gurbin gasar zakarun Turai

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Bayan shekara 20 a jere da Arsenal ke buga gasar zakarun Turai, ta kasa samun damar buga wadda za a yi a badi

A karon farko Arsenal ta kasa samun tikitin shiga gasar cin kofin zakarun Turai ta badi duk da doke Everton 3-1 da ta yi a ranar Lahadi a wasan karshe na gasar Premier.

Arsenal wadda sau 20 tana zuwa gasar zakarun Turai din ta kammala wasannin Premier ta bana a mataki na biyar, bayan da ta yi wasanni 38 ta ci 23 ta yi canjaras 6 aka doke ta sau 9.

Kungiyar da ke birnin Landan ta ci kwallo 77 aka zura mata 44, yayin da ta hada maki 75, wanda hakan ke nufin Arsenal za ta buga gasar kofin Europa na badi kenan.

Chelsea ce ta lashe kofin bana kuma na shida jumulla sai Tottenham ta biyu Manchester City ta uku, inda Liverpool ce ta hudu.

Kungiyoyi uku da suka kasa kai bantensu a gasar bana sun hada da Hull City da Middlesbrough da Sunderland, wadanda za su koma buga Championship a badi.

Labarai masu alaka