Switzerland za ta daina amfani da lantarkin nukiliya

Switzerland nuclear plant Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Tun a shekara ta 2011 ne gwamnatin Switzerland ta fara tunanin rufe tashoshin lantarkinta na nukiliya

Al'ummar Switzerland sun kaɗa ƙuri'ar daina amfani da lantarkin nukiliya, inda gwamnatin ƙasar za ta maye gurbinsa da na makamashi mai tsafta.

Fiye da kashi 58 cikin 100 ne suka goyi bayan matakin samar da lantarki daga hanyoyi masu tsafta a wani zaɓen raba gardama da aka yi ranar Lahadi.

Switzerland na da tsoffin tashoshin lantarki na nukiliya guda biyar da ke bai wa ƙasar kashi ɗaya cikin uku na makamashin da take buƙata.

Ya zuwa yanzu, ba a sanya ranar rufe tasoshin ba, amma dai ƙasar za ta mayar da hankali wajen bunƙasa hanyoyin samun lantarki daga hasken rana da iska da kuma ruwa.

Masu adawa sun yi gargaɗin cewa matakin daina amfani da makamashin nukiliya zai kawo tsawwalar farashin lantarki da kuma ɓata shimfiɗar ƙasa.

Sai dai shugabar jam'iyyar Green Party mai rajin kare muhalli a Switzerland, Regula Rytz, ta yaba wa ƙuri'ar a matsayin wani "muhimmin sauyi na tarihi".

"Al'ummar Switzerland sun ce a'a ga matakin gina sabbin tashoshin nukiliya na lantarki kuma eh ga bunƙasa hanyoyin samar da makamashi mai tsafta," ta nanata.

Gwamnatin Switzerland ta fara tunanin daina amfani da makamashin nukiliya inda za ta koma ga makamashi mai tsafta bayan lalacewar tashar Fukushima ta ƙasar Japan yayin ambaliyar tsunami a shekara ta 2011.

Zaɓen raba gardaman a yanzu ya share mata hanya don ci gaba da shirinta wanda zai fara a farkon shekara ta 2018.