Kiran Buhari ya yi murabus ya janyo ɓaraka

Buhari da Osinbajo Hakkin mallakar hoto PRESIDENCY
Image caption Aisha Yesufu ta buƙaci Buhari ya yi murabus don bai wa mataimakinsa damar shugabantar Nijeriya saboda rashin lafiyar da ke samunsa

Wasu 'ya'yan ƙungiyar BringBackOurGirls mai rajin ceto 'yan matan sakandaren Chibok sun buƙaci wata jagorarsu Aisha Yesufu ta sauka daga muƙaminta.

Kiran dai ya biyo bayan wani bidiyo da jagorar ta fitar ne a makon jiya, wanda ya karaɗe shafukan sada zumunta inda ta roƙi shugaban Nijeriya, Muhamadu Buhari ya sauka daga kan mulki saboda rashin lafiyarsa.

Sai dai a martaninta, Aisha Yesufu ta ce maganar da ta yi ta ƙashin kanta ce amma ba da sunan ƙungiya ba.

Wani ɗan ƙungiyar, Waziri Bello ya ce rayukan 'yan Bring Back Our Girls da dama sun ɓaci da wannan bidiyo da jagorar ta fitar.

A cikin bidiyon wanda mutane suka yi masa caaa! An ga Aisha Yesufu na kira ga shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya yi Allah da Ma'aiki ya sauka daga mulki don bai wa mataimakinsa cikakkiyar dama.

Image caption A cikin bidiyon Aisha Yesufu ta yi suka kan yadda harkoki suke tafiya a gwamnatin Buhari

Ta ce harkoki ba sa gudana a gwamnati don kuwa Farfesa Yemi Osinbajo a matsayinsa na muƙaddashin shugaba yana da iyaka.

Ta ba da misali da wasu batutuwa ciki har da kasafin kuɗin shekara 2017 wanda ta ce ya gamu da tarnaƙi saboda rashin lafiyar shugaba Buhari.

Waziri Bello ya ce ko da yake, Aisha Yesufu ta nuna cewa kiran da ta yi wa shugaba Buhari ya sauka ra'ayinta ne na ƙashin-kai amma ba da sunan ƙungiya ba, duk da haka suna taƙaddama da wannan.

"Ba yadda za a yi ta zo ta yi magana irin wannan kuma ta ce za a iya raba wannan magana da matsayinta (na ƙungiyar), in ji shi.

"Ba mu yarda da wannan magana ba. A matsayinta na shugaba. Ba za ka ga laifin mutane ba, idan sun ce ƙungiyarmu ce ta yi wannan magana."

Image caption Shugaba Muhammadu Buhari ya sha nanata ƙudurinsa na tabbatar da ceto 'yan matan Chibok

Ɗan ƙungiyar ya kuma yi Allah wadai da kiran na Aisha Yesufu.

Ya kuma yi kira gare ta da ta sauka daga jagorancin ƙungiyar idan tana son shiga harkokin siyasa.

A cewarsa ranar Asabar kamata ya yi ta zama abar murna don kuwa a ranar ce iyayen 'yan matan sakandaren Chibok suka gana da 'ya'yansu 82 da gwamnatin Buhari ta yi dalilin kuɓutarsu.

"Ai in duk Nijeriya za su ce ya sauka, ya kamata a ce ita ko kuma mu ƙungiyarmu ta ce a'a. Tun da ya ceto mana yaranmu 106 da kuma sauran dubban mutane daga hannun Boko Haram. Ya kamata a ce an ba shi dama don ya ci gaba da wannan kyakkyawan aiki da ya yi mana alƙawari."

Image caption Bidiyon Aisha Yesufu ya zo ne a daidai lokacin da 'yan matan Chibok 82 suka gana da iyayensu bayan shafe tsawon shekara uku a hannun Boko Haram

Ita dai jagorar ta ce: "Ba ruwan BBOG a ciki. Magana ce ta Aisha Yesufu, da take da 'yancin kanta, na yin magana a ƙasar Nijeriya."

A cewarta, ba ta ga dalilin da ya sa wasu ke kumfar baki da kalamanta ba, don kuwa shi ma da kansa shugaba Buhari a cewarta ya faɗa wa wani shugaban ya sauka daga mulki a lokacin da yake cikin halin rashin lafiya.

Da aka tambaye ta ko ta shiga siyasa ne ya sa take furta irin waɗannan kalamai. Sai Aisha ta ce: "Sai ɗan siyasa ne kawai yake da bakin magana?"

Ta ce ita ba ta shiga siyasa ba, amma idan tana son yin haka, babu wanda yake da ikon hana ta.

Labarai masu alaka