An tsare tsohon shugaban Barcelona

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sandro Rosell ya ja ragamar Barcelona daga 2010 zuwa 2014

'Yan sanda a Spaniya sun tsare tsohon shugaban kungiyar kwallon kafa ta Barcelona Sandro Rosell kan binciken halasta kudin haram.

Haka kuma an damke wasu mutanen bayan da jami'an tsaro suka kai sumame wasu ofisoshi tara da gidaje a yammacin Catalonia.

Rosell wanda ya shugabanci Barcelona daga shekarar 2010 zuwa 2014, ya yi murabus bayan da wata kotu a Spaniya ta amince a binciki cinikin Neymar daga Santos zuwa Barca a 2013.

A watan Yunin 2016, Barcelona ta biya tarar fam miliyan 4.7 kan cinikin Neymar, an kuma zargi kungiyar da kin biyan haraji, wanda ta karyata hakan.

Mai dakin Rosell tana daga cikin mutanen da jami'an tsaro suka damke a ranar Talata.