Nigeria: 'Za mu daina sayo tataccen mai daga waje'

Ministan mai na Nijeriya Emmanuel Ibe Kachikwu Hakkin mallakar hoto Twitter
Image caption Nijeriya ta yi alƙawariin samun wadatar man fetur daga shekara ta 2019

Ministan albarkatun man fetur na Nijeriya, Ibe Kachikwu ya dauki alkawarin cewa matuƙar gwamnatinsu ta gaza kawo ƙarshen al'adar shigo da man fetur daga waje a ƙarshen shekara ta 2019, to zai sauka daga mukaminsa.

Allah ya albarkaci Nijeriya da ɗumbin arzikin man fetur, inda take fitar da dubban ɗaruruwan ganga ta ɗanyen man, amma kuma sai ta ɓuge da sayen tatacce daga waje saboida rashin ingantattun matatun tacewa a ƙasar..

Da yake hira ta musammam da BBC, Mr. Kachikwu ya ce zai bar muƙaminsa matuƙar gwamnatinsu ba ta iya kawo ƙarshen al'adar sayen tataccen man da take buƙata daga waje ba a shekara ta 2019.

Sai dai, gwamnatin tasu za ta kammala wa'adinta na farko ne a tsakiyar shekarar da ministan yake fatan wadatar da tataccen man fetur ga 'yan Nijeriya, ko da yake, jagoran gwamnatin na da damar sake tsayawa takara bisa tanadin tsarin mulki.

"Akwai bukatar mu rika sarrafa danyen mai a maimakon mu rika fitar da shi waje, kuma ƙoƙarinmu ya yi nisa wajen inganta matatunm na man fetur."

Kachiku ya ce: "Na kudiri aniyar cewa Nijeriya za ta samu wadatar man fetur nan da shekara ta 2019.

Ministan ya ce tsagerun matasa a yankin Niger Delta, sun haifar da lalacewar bututan man fetur da kuma nakasu ga ayyukan haƙar danyen mai.

Ya ce a baya Nijeriya tana haƙo gangar danyen mai miliyan biyu da dubu dari biyu, amma ayyukan waɗannan tsageru ya janyo raguwarsa zuwa ganga miliyan daya da dubu dari biyu.

"Ba karamin aiki ba ne a gabanmu kafin harkokin hako man fetur su fara ingantuwa."

"Za mu ci gaba da mai da hankali kan wannan al'amari, ta yadda ba zai haifar da tarnaki ba, don samar wa tattalin arzikin Nijeriya alkibla.

Mr Ibe Kachuku ya ce muradin gwamnati shi ne nan gaba ta iya hako gangar danyen mai miliyan uku ko miliyan uku da dubu dari biyar.

Ya kuma ce rashin tsare-tsare da za a dade ana cin gajiyarsu ne a bangaren albarkatun man fetur din ne ya sa al'amuran suka kara tabarbarewa.

Labarai masu alaka