Ka san auren da rashin ganin miji bai yanke ƙauna ba?

Mata da yara a kasar Ghana Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mazaje kan tafi ci-rani ƙasashen Turai su bar matansu tsawon shekaru a Ghana suna fama da ɗawainiyar 'ya'ya

Wasu matan aure a Ghana na bayyana damuwa kan yadda suke shafe shekara da shekaru ba tare da sun sa mazajensu a ido ba. To me ya sa? Ina mazajen nasu ke zuwa?

Matan dai kan yi wani aure ne da ake kira auren nesa ko kuma boga, nau'in aure ne da 'yan Ghana masu ci-rani a ƙasashen Turai ke yi a wasu lokuta ma matar ba ta taɓa ganin mijinta ba.

Akwai waɗanda kan yi auren bayan wani ɗan zama na taƙaitaccen lokaci a Ghana sai kuma mijin ya sa ƙafa ya fice, ko da yake, zai dinga aiko mata da kuɗin abinci da na sauran buƙatun rayuwa.

Sukan tafi ci-ranin ne da zimmar samun takardun zama, da kuma ayyukan yi, su bar matan tsawon shekaru ba tare da waiwayar gida ba.

Malama Samira Abdulrazak ta ce shekara uku suka yi suna soyayya kafin su yi aure, ko da yake, ba su taɓa ganin juna ido da ido ba.

Ta ce sukan yi tattauna ta wayar tarho da mijinta da ke zaune a can ƙasashen Turai.

"Ban taba ganinsa ba, amma yana aiko min da dala ɗari zuwa ɗari biyu a kowanne wata."'

Ta ce abu ɗaya ne ya dame ta game da kewar mijinta, amma yakan ba ta haƙuri cewa yana neman takardar iznin zama ne a ƙasar Turai don sama musu rayuwa mafi inganci.

Samira ta ce a yanzu shekara hudu kenan da yin aurensu.

"Wani lokaci nakan shiga damuwa, nakan riƙa mafarkin jima'i, idan na faɗa masa sai ya ce na ƙara haƙuri da zarar ya samu takarda zai zo gare ni."

Ita ma wata da ba ta bayyana sunanta ba a birnin Accra ta ce sun kai shekara 14 da mijinta shi yana Turai, ita tana Ghana.

Ta ce Allah ya albarkaci aurensu da ɗa biyu, amma ba ta jin kewa sosai saboda 'ya'yanta sun kore mata.

"Bayan tafiyarsa Turai sai da ya shafe shekara bakwai kafin ya dawo gida, kuma da ya zo din ma wata uku ya yi sai ya koma."

Wani malamin addinin musulunci a Ghana, Malam Abdulrahman ya ce irin wannan auren nesa ba shi da amfani ko kadan a musulunci.

Ya ce aure abu ne mai matukar muhimmanci a addinance da bai kamata a yi wasa da shi ba.

'"Allah ya ce aure babu abin da yake haifarwa sai soyayya da tausayawa, amma in har za ka tafi ka bar matarka tsawon lokaci ya zamto take haƙƙi kenan."

Galibi dai wasu na kallon irin wannan aure a matsayin kwadayin neman abin duniya ne ba wai saboda soyayya ba.