Wasu sun yi liyafa da naman shanu a Indiya

India Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mabiya addinin Hindu a India suna girmama shanu

Masu adawa da gwamnatin India a jihar Kerala, sun gudanar da liyafa da naman shanu a cikin unguwanni, sannan suka yi maci dauke da kan bauna, domin nuna rashin jin dadinsu da karin matakai na rage yawan naman ci a kasar.

A karkashin sababbin dokokin, shanu, wadanda mabiya addinin Hindu ke girmamawa sosai, an hana sayar da su a kasuwa domin yankasu.

Haka ma suma baunaye da rakuma, an hana sayar da su a kasuwa domin yanka, duk da cewa su din ba dabbobi ba ne da ake girmamawa.

Shugabanni a jihohin da a ka fi mu'amala da nama, sun ce wannan wata babbar barazana ce ga sana'o'in makiyaya, da masu sana'ar sayar da nama, waddanda akasarinsu Musulmai ne marasa rinjaye.