Korea ta Arewa ta harba makami mai linzami na 9 a bana

Korea ta Arewa Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A karo na uku cikin makonni uku Korea ta Arewa ta yi gwajin makami mai linzami

Koriya ta Arewa ta sake harba makami mai linzami da ke cin gajeren zango cikin tekun Japan, karo na uku a cikin mako uku.

Matakin dai ya zafafa zaman ɗar-ɗar ɗin da ake fama da shi a yankin tekun Koriya, inda ta bijirewa yunƙurin ƙasashen duniya na yi wa shirin nukiliyarta shamaki.

Gwajin makamin, wanda shi ne tara a wannan shekara ya janyo Allah wadai cikin gaggawa.

Fira ministan Japan Shinzo Abe ya ce taron manyan ƙasashen da suka fi bunƙasar tattalin arziƙi a duniya G7 ya amince da bai wa batun Koriya ta Arewa ƙololuwar fifiko.

Ya ce Japan za ta yi aiki da sauran ƙasashe kamar Amurka don ɗaukar matakan da za su hana hukumomin birnin Pyongyang ci gaba da takalar faɗa.

Rundunar sojin Amurka da ke yankin Pacific ta ce an harba makami mai linzamin ne daga birnin Wonsan na Korea ta Arewar, kuma ya yi tafiyar minti shida a sararin samaniya kafin ya sauka.

Babban sakataren hukumar gudanarwar ƙasar Japan Yoshihide Suga ya shaida wa manema labarai cewa makamin ya sauka a wani yanki da ke tsakanin tsibirin birnin Sado da kuma tsibirin Oki na kasar Japan din.

Labarai masu alaka