Kun san maganin kashe kwayoyin cutar da ka iya ceton rayuka?

Amurka
Image caption Sabon launin maganin kashe kwayoyin cutar ka iya ceto rayuka da dama in ji kwararru

Masana kimiyya sun yi bajintar ƙirƙiro wani sabon launin maganin kashe ƙwayoyin cuta, da ka iya ceto rayukan ɗumbin al'umma.

Sun ce binciken zai inganta yaƙin da suke yi da cutuka masu bijire wa magunguna - ɗaya daga cikin babbar barazana ga lafiyar al'ummar duniya.

Masu bincike sun jirkita rukunin ƙwayar atom na wani magani mai suna Vancomycin inda ƙarfinsa ya ninka har sau kusan dubu guda.

Maganin ka iya far wa ƙwayar cuta ta fuska uku, abin da zai zame mata mai matuƙar wahala ta samu kuzarin rama faɗa.

Dr. Dale Boger na cibiyar Scripps a California shi ne jagoran masu wannan nazari.

Ya ce "Sauyin da muka yi masa, zai kasance abu mai wahala ƙwayar cuta ta iya bijirewa wannan magani."

Alƙaluma sun ce irin waɗannan cutuka na haddasa mace-mace kimanin dubu 50 duk shekara a Amurka da Turai.

Labarai masu alaka