Ko ina 'yan adawar hukumomin Borno suka shiga?

Gwamnan jihar Borno Kasheem Shettima Hakkin mallakar hoto Borno state government
Image caption 'Yan adawar Borno sun gudu sun tare Abuja da Kano da Kaduna in ji gwamna Shettima

Gwamnan Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, Kashim Shettima ya zargi 'yan adawar jihar da tafka ƙeta da makirci bayan sun gudu sun bar Borno.

Jihar Borno ita ce ta fi fama da hare-haren ƙungiyar 'yan ta-da-ƙayar-baya ta Boko Haram.

A cewar Kashim Shettima na jam'iyyar APC, 'yan adawar gwamnatinsa duk sun gudu sun tare a Abuja da Kano da kuma Kaduna.

"Kin san ɗan adawa ba abin da za ka yi, ya yaba maka. Mafi yawansu ba sa Maiduguri, sun gudu da karnukansu da kyawoyinsu da gidajensu duka sun gudu... Suna makirce-makircensu."

Ya ce su 'yan adawa, idan ba a ƙeta da makirci ba, ba abin da suka sa a gaba ba, musammam 'yan adawar Borno.

Ya yi iƙirarin cewa wasunsu shekara huɗu kenan rabonsu da Borno.

Kashim Shettima na mayar da martani ne kan zargin sace kuɗaɗen ƙananan hukumomi da ake yi wa gwamnatinsa.

A cewarsa nawa ƙananan hukumomin jihar suke samu da har za a yi batun sacewa? Yawanci sai an tallafa musu kafin ma su iya biyan albashin ma'aikatansu, in ji shi.

Ya ce gaskiya batun shi ne babu wanda yake danne kuɗin ƙananan hukumomi, kuma kuɗin da suke samu a baya, yanzu ba sa samunsu. Baya ga sansanonin 'yan gudun hijira da suke da su a Maiduguri.

Labarai masu alaka