Hotunan yadda Igbo suka tsayar da al'amura don Biafra

Rahotanni daga Kudu maso Gabashin Najeriya na cewa al'amura sun tsaya cak a wasu manyan biranen yankin don nuna hadin kai ga fafutukar kafa yankin Biafra

Biafra
Bayanan hoto,

Kungiyoyin IPOB da MASSOB sun yi wannan kiran cewa mutane su zauna a giadajensu don tunawa da shekara 50 na fara fafutukar kafa yankin Biafra da marigayi Chukwuemeka Ojukwu ya yi.

Bayanan hoto,

A ranar 30 ga watan Mayun shekara 1967 masu fafutukar kafa Biafra suka ayyana ballewa daga Najeriya.

Bayanan hoto,

Babu wani rahoto na tashin hankali

Bayanan hoto,

Dukkan sauran jihohin yankin ma ana cikin irin wannan yanayi. Yankin Kudu maso Gabas dai ya kunshi jihohin Anambra da Enugu da Abia da Imo da kuma Ebonyi.

Bayanan hoto,

Galibin masu fafutukar 'yan kabilar Igbo ne da ke yankin kudu maso gabashin Najeriya.

Bayanan hoto,

Tuni aka jibge jami'an tsaro a muhimman wurare da ke jihohin yankin.

Bayanan hoto,

Masu fafutukar suna zargin cewa ana mayar da su saniyar ware a al'amuran tafiyar da Najeriya

Bayanan hoto,

Sai dai kuma ana ci gaba da harkokin sufuri a yankin.

Bayanan hoto,

A birnin Anacha na jihar Anambra kuwa, harkokin da suka hada da na kasuwanci da sufuri da makarantu da bankuna duk sun kasance a rufe.