Masu bincike sun gano 'fadamar' kudi

Wani rukuni na masu bincike a Rasha sun gano kudin tsohuwar tarayyar Sobiyet da aka kiyasta sun kai rouble biliyan daya a cikin wani tsohon wurin da ake hakan ma'adinai. Amma kudaden basu da sauran amfani a yanzu.

Daya daga cikin 'yan rukunin Abandoned Country na rike da kudin zamanin tsohuwar tarayyar Sobiyet

Asalin hoton, YouTube/Abandoned Country

Bayanan hoto,

Wasu daga cikin tsofaffin kudaden da aka gano a tsohuwar mahakar ma'adinai kusa Moscow

Jaridar Komsomolskaya Pravda ta ruwaito a shafinta na yanar gizo cewa rukunin masu binciken sun fito ne daga garin Saint Petersburg, kuma su kan wallafa bayanai game da wuraren da suka zame kufai a cikin kasar Rasha. Jaridar ta ce sun gano kudin ne bayan sun sami labarin an jibge kudi a wani tsohon wurin ajiyar bama-bamai masu linzami kusa da birnin Masko gabanin faduwar tsohuwar tarayyar Sobiyet. Bayan da rukunin masu binciken suka shafe awoyi suna tafiya a yanayi mara kyau cikin yankin Vladmir na Rasha, sun isa wurin dake cike makil da kudi.

Sun sami kudin da yawansu ya kai rouble biliyan daya (dalar Amurka miliyan 18 a darajar kudin yanzu, ko dala miliyan 33.3 a karshen mulkin Sobiyet a 1991). Kudaden manya da kanana, an yi amfani dasu ne tsakanin 1961 zuwa 1991, kuma basu da daraja a kasar Rasha yanzu.

Tashar YouTube ta rukunin masu binciken ta nuna yadda ambaliyar ruwa a wurin a shekarun baya ya mayar da wurin tamkar fadamar kudade masu hoton tsohon shugaba Vladmir Lenin.

Wasu tsofaffi mazauna yankin ne suka shaida ma masu binciken labarin wurin amma sun ce babu mai zuwa wurin domin suna tsoron shakar iska mai guba daga tsofaffin kayan yaki. Amma da aka gwada iskar wurin da na'urar Geiger sai aka tabbatar babu hadarin shiga wurin.

Akwai sauran kudin da ba a gano ba?

Madugun rukunin masu binciken, Olga Bogdanova ta ce babu kalaman da zasu iya bayyana yawan "arzikin" dake wurin. "Ga murna ga bakin ciki saboda ka san wannan wani karni ne da ya riga ya wuce har abada, kuma wannan kudin ya ishi kowane mutum", in ji ta. Rouble 100 albashi ne mai tsoka a lokacin mulkin Sobiyet.

Tashar Talabijin ta Rossiya1 tayi hira da abokan aikinta Anton Alekseev da Sergey Volkov, inda mai gabatarwa ya bayyana cewa an jibge kudin ne bayan odar da tsohuwar gwamnatin Sobiyet ta bayar na yin haka, kuma wannan na daya daga cikin wurare uku a cikin Rasha da aka jibge irin wannan kudin.

Asalin hoton, YouTube/Abandoned Country

Bayanan hoto,

Anton Alekseev a kan jikakkun tsofaffin damin kudaden tsohuwar tarayyar Sobiyet

Masu shiga zaurukan zumunta da dama sun bayyana sha'awarsu, inda wasunsu suke fatar da zasu iya kashe kudin. "Kawai fadawa zanyi cikin wurin kamar Scrooge McDuck," in ji wani. Wani kuma cewa yayi "kash! Da zan iya mayar da lokaci baya, da na debo kudin kuma da na sayi hannayen jari masu yawa a kamfanonin Google da Gazprom da Rosneft, kaga da ban sake yin aiki ba kenan duk tsawon rayuwata."