An kai harin bam yayin jana'iza a Afghanistan

Mutane sun yi takansu bayan tashin bam din yayin jana'izar Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Mutane sun yi takansu bayan tashin bam din lokacin jana'izar

Wasu bama-bamai uku sun tashi yayin da ake jana'izar wani mutum a birnin Kabul na kasar Afghanistan, inda suka kashe mutum shida kuma suka jikkata wasu da dama, kamar yadda hukumomi suka bayyana.

Harin ya faru ne yayin janai'izar dan wani sanata da ya mutu lokacin wata zanga-zangar da aka yi ranar Juma'a.

An kira zanga-zangar ne saboda zargin da mazauna birnin suke na cewa gwamnati na nuna halin ko in kula game da hare-haren da ake kai wa birnin.

Sai dai hukumomi a kasar sun gargadi mutane kan su guji shiga zanga-zanga saboda yiwuwar harin masu tada kayar baya.

Har yanzu ba a san abin da ya jawo fashewar bama-baman ba tukuna, kuma babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai sa.

Akalla mutane 87 ne suka ji raunuka, kamar yadda ministan kiwon lafiyar kasar ya bayyana. Kodayake wasu rahotanni na cewa adadin wadanda suka mutu zai iya zarta shida.

Harin shi ne na uku da aka kai Kabul a cikin kwana hudu. Mazauna birnin ba su gama murmurewa daga harin da aka kai ba a farkon makon nan, wanda ya kashe fiye da mutum 90.

An sanya shinkayen bincike a tsakiyar birnin Kabul kuma akwai motocin jami'an tsaro da suke sintiri a kan hanyoyin birnin, a wani mataki na tabbatar da tsaron rayuka da kuma dukiyar al'umma.

Labarai masu alaka