Marocco za ta zama mamba a ƙungiyar Ecowas

Sarki Mohammed na Morocco

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Sarki Mohammed na kokarin gyara alakar kasarsa da kasashen Afirka

Kungiyar kasashen Yammacin Afirka ta Ecowas ta amince da ta karbi Moroko a matsayin mamba duk da cewa kasar na yankin Arewacin Afirka.

To sai dai shugabanin kungiyar ta Ecowas a taron su na Liberia sun ce da akwai bukatar duba yanayin Moroko kafin ta shigo cikin kungiyar.

Sarki Mohammed bai halarci taron ba sabili da gayyatar da aka yi wa Fira Ministan Israila Benjamin Netanyahu.

Moroko ta nemi shiga kungiyar ta Ecowas bayan shigarta kungiyar Tarrayar Afirka a watan Januari.

Kasar ta fice daga kungiyar tarrayar Afirka ne a 1984 bayan da aka tabbatar da yankin Yamacin Sahara a matsayin wani yanki mai cin gashin kai.

Moroko na ganin cewa yankin Yammacin Sahara wani bangare ne na kasar Moroko a cikin tarihi.

Moroko ta shafe shekara 30 na baya-bayan nan tana karfafa huldarta da kashen Turai tare da bunkasa dangantakarta da Afirka.

Yadda Morocco ta yi nisa da sauran kasashen kungiyar Ecowas: