Jiragen saman Qatar za su daina ratsawa ta Masar da Saudia

Jirgin saman Qatar Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Harkokin sufurin sama na kasar Qatar za su samu nakasu saboda takukumin kasashen

Za a dakatar da jiragen saman kasar Qatar bi ta sararin samaniyar kasashen Masar da Saudia, yayin da cigaba da takun sakar ke barazana da manyan harkokin sufurin sama.

Kasashe da dama ne dai suka yanke hudda da Qatar din kan zargin tallafawa ayyukan ta'addanci a yankin.

Qatar din ta musanta zargin marawa 'yan ta'addar baya da suka hada da kungiyar IS, ta kuma ce matakin ba shi da tushe.

Ma'aikatar harkokin wajen kasar Sudan ta nuna aniyarta ta shiga tsakanin bangarorin biyu, don kwantar da hankula da sasantawa.

Wannan gagarumar rarrabuwar kawuna tsakanin manyan kasashen yankin Gulf da aminan juna ne, na zuwa a yayin da ake takun saka tsakanin yankin da kuma makwabciyarsu kasar Iran.

Saudiyya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da kuma Bahrain, sun bai wa duka 'yan kasar Qatar da suke zaune a ƙasashensu wa'adin mako biyu da su fice daga ƙasashensu.

Hakazalika, ƙasashen uku sun haramta wa 'yan ƙasarsu zuwa ƙasar Qatar. Sun kuma haramtawa 'yan kasarsu zuwa kasar ta Qatar.

Sai dai Saudiyya ta ce ba za ta hana alhazan Qatar halartar aikin hajjin bana ba.

Kasashen Hadaddiyar Daular Larabawa da Masar sun bai wa jami'an huddar jakadancin Qatar din sa'oi 48 su fice daga kasashen biyu.

Labarai masu alaka