Dakarun haɗin gwiwa na Sahel za su samu tallafin EU

Dakarun Faransa Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A watan da ya gabata ne shugaban Faransa Emmanuel Macron ya ziyzrci dakarun Faransar a kasar Mali

Kungiyar Tarayyar Turai ta amince da samar da fiye da dala miliyan hamsin ga sabuwar rundunar haɗin gwiwar Afirka a yankin Sahel.

Rundunar za ta ƙunshi dakaru daga ƙasashen Mali da Mauritania da Chadi da Burkina Faso da kuma Nijar, don yaƙi da ƙungiyoyi masu da'awar jihadi, da harkokin fasa-ƙwauri da kuma baƙin haure.

Ministan harkokin wajen Mali, Abdoulaye Diop ya sanar da cewa za a kafa rundunar ce da dakaru kimanin dubu na sojoji da 'yan sanda, ƙari a kan shirin baya na dakaru dubu biyar.

Ana sa ran rundunar za ta fara aiki a ƙarshen wannan shekara.

Babban aikinta shine yakar kungiyoyin masu jihadi dake da karfi a yankunansu, har ma da masu fataucin mutane.

Sahel yanki ne na kungiyoyi masu tsattauran ra'ayin addinin Islama da dama, da wasu ke da alaka da kungiyar al-Qaeda.

Dakarun Faransa fiye da 3,000, da dakarun Majalisar Dinkin Duniya 12,000 ne ke fafatawa a kasar Mali tun a shekara ta 2013, lokacin da Abzinawa 'yan tawaye ke jagorantar ayyukan tayar da kayar baya a arewacin kasar.

An fatattaki 'yan tawayen, amma kuma sun cigaba da kai munanan hare-hare kan dakarun wanzar da zaman lafiya a arewaci da tsakiyar yankunan.

Ayyukan wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya daya daga cikin mafi hadari ne a cikin shekaru da dama, inda aka hallaka dakarunta fiye da 115 cikin shekaru hudu.

Tashin hankalin ya bazu zuwa kan iyakar kasashen Burkina Faso da Ivory Coast, inda ake kai wa baki 'yan yawon bude ido farmaki a cikin shekarun baya-bayan nan.