Kamfanin sufuri na Uber ya mayar wa fasinjoji kudade

Uber London Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Manhajar Uber

Kamfanin Uber ya mayar wa fasinjojin da suka yi amfani da manhajar kamfanin a kusa da gadar da aka kai harin ta'addanci na birnin Landan.

Kamfanin sufurin ya sha suka daga jama'a a zaurukan zumunta na intanet saboda kyale kudin mota ya tashi a lokacin harin wanda aka kai da misalin karfe 10 na dare.

Kamfanin ya soke tashin farashin bayn wani lokaci matakin da ya sa kudin motar ya koma yadda aka saba.

An kashe mutane bakwai lokacin da wasu mutane suka tuka wata motar daukan kaya cikin jama'a a kan gadar birnin Landan kana suka farma wasu mutanen da wukake.

'Yan sanda sun harbe maharan har lahira cikin mintuna takwas da samun rahoton harin.

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Wani jirhgi mai saukan angulu ya sauka a bisa gadar ta Landan bayan harin ta'addancin

Idan akwai fasinjoji fiye da motocin haya a wani wuri, manhajar ta Uber kan kara kudin motar da za'a biya.

Wannan ya sa kudin motar ya tashi a daidai lokacin da mutane ke kokarin gudu daga wurin saboda sun fi motocin tasi yawa.

"Bayan da muka sami labarin an kai harin sai muka dakatar da tsarin karin kudin mota a dukkan yankunan da harin ya shafa", in ji Tom Elvidge babban jami'in kamfanin dake birnin Landan a wata sanarwa da kamfanin ya fitar ranar Lahadi.

"Kuma mun tabbatar da bamu karbi kudin kowa ba daga wurin harin, in ji shi.

Kamfanin Uber ya ce an dakatar da tashin kudin motar da misalin karfe 10:50 na dare, kuma an fadada dakatarwar zuwa yankin tsakiyar birnin Landan zuwa karfe 11:40 na daren.

Kamfanin ya kara da cewa an riga na mayar wa mutanen da suka yi amfani da manhajar ta Uber a yankin da harin ya shafa kudadensu.

Amma idan ba a maida ba, wadanda wannan lamarin ya shafa na iya tuntubar kamfanin.

An yaba wa direbobin bakaken motocin tasi na birnin Landan saboda daukar mutane kyauta da suka yi domin raba su da wurin harin.

Kamfanin Uber ma ya tallata wa mazauna birnin Manchester irin wannan damar ta shiga mota kyauta bayan harin da aka kai a Manchester Arena ranar 22 ga watan Mayu.

Kamfani kuma ya sha alwashin mika wa kungiyar Red Cross kudaden motar da ta karba na wadanda suka shiga motocin da suka ji jigilar 'yan kallon bikin waka na One Love Manchester.

Labarai masu alaka