Shooting Stars za ta kara da Kano Pillars

Hakkin mallakar hoto NPFL Twitter
Image caption Kano Pillars tana mataki na 12 a kan teburin Firimiyar Nigeria

Kano Pillars za ta ziyarci Shooting Stars domin karawa a wasan mako na 23 a gasar cin Kofin Premier Nigeria a ranar Laraba.

Kano Pillars wadda ta ci Lobi Stars 2-1 a ranar Lahadi tana mataki na 12 a kan teburi da maki 30, ita kuwa Shooting Stars tana matsayi na 19 da maki 25.

Ga wasu daga cikin wasannin da za a yi:

  • Lobi Stars da Mountain Of Fire And Miracles
  • Ifeanyi Ubah da Abubakar Bukola Saraki
  • Niger Tornadoes da Rivers United FC
  • El-Kanemi Warriors da Enugu Rangers
  • Abia Warriors da Remo Stars
  • Gombe United da Enyimba International
  • Sunshine Stars da Plateau United
  • Nasarawa United da Katsina United

Labarai masu alaka