Rashin aiki ya karu a Nigeria da kashi 2 %

Wata 'yar bautar kasa a Nigeria Hakkin mallakar hoto PIUS UTOMI EKPEI
Image caption Rahoton ya kara da cewar haka ma rashin aikin ya fi yawa ga maza fiye da mata

Hukumar kula da kididdiga ta Najeriya ta ce yawan marasa aikin yi a kasar ya karu da fiye da kashi biyu cikin dari a rubu'in karshe na shekarar bara.

Wannan na nufin adadin marasa aiki a kasar ya kai mutane miliyan goma sha daya da rabi, abin da ke daidai da kashi 14% na mutanen da ke iya aiki a kasar.

Alkaluman da hukumar ta National Bureau of Statistics ta fitar sun nuna cewa matsalar rashin aikin tafi shafuwar matasa ne wadanda shekarunsu suka kama daga 15 zuwa 34.

Haka ma ko baya ga rashin aiki sam-sam, akwai kuma matsalar samun ayukkan da ba su dace da kwarewa ko matsayin wasu ma'aikatan ba wadda ta ce fiye da kashi 21% na masu ayukkan yi a kasar ne ke fama da irin wannan matsalar.

Sai dai rahoton bai bayyana dalilan da suka kawo karuwar rashin ayyukan a kasar ba, amma dai a bara din ne kasar ta shiga cikin halin karayar arziki mafi muni cikin shekaru 20 sakamakon faduwar farashin danyen mai wanda shi ne babbar hanyarta ta samun kudaden shiga.