Ronaldo ya fi kowa karbar kudi a wasanni

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ronaldo ya ci kofin Zakarun Turai a karawar da Real Madrid ta doke Juventus 4-1

Dan wasan Real Madrid, Cristiano Ronaldo, ya ci gaba da zama a matsayi na daya a wanda ya fi karbar albashi a tsakankanin masu wasanni a duniya in ji mujallar Forbes.

A bara Ronaldo ya karbi fam miliyan 72.05 kudin albashi da ladan wasanni da tallace-tallace da ya yi, amma a bana ya samu karin fam miliyan 3.87.

Cikin jadawalin da Forbes ta fitar 'yan wasa 11 ne daga wasanni daban-daban suke kan gaba a wajen samun kudi.

Masu wasan kwallon kwando su 32 ne suke cikin 100 farko, sai masu buga kwallon baseball 22 da 'yan wasan zari-ruga na Amurka 15 da masu taka-leda tara.

Ga jerin 'yan wasa 10 da suka fi samun kudin a duniya:

  1. Cristiano Ronaldo - kwallon kafa ($93m/£72.05m)
  2. LeBron James - kwallon basketball ($86.2m/£66.79m)
  3. Lionel Messi - kwallon kafa ($80m/£61.98m)
  4. Roger Federer - kwallon tennis ($64m/£49.58m)
  5. Kevin Durant - kwallon kwando ($60.6m/£46.95m)
  6. Andrew Luck - zari-ruga ($50m/£38.74m)
  7. Rory McIlroy - kwallon golf ($50m/£38.74m)
  8. Stephen Curry - kwallon kwando ($47.3m/£36.64m)
  9. James Harden - kwallon kwando ($46.6m/£36.10m)
  10. Lewis Hamilton - tseren motoci a($46m/£35.64m)

Labarai masu alaka