Cameroun: Kungiyar Bakandamiya na kwace wayoyin salula a hannun 'yan mata

Wata budurwa na duba wayarta ta hannu tare da kawarta Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wasu 'yan mata na duba wayar hannu

Kungiyar Bakandamiya reshen garin Touroua ta fitar da wasu matakai domin dawo da tarbiyyar 'ya'ya mata.

A cikin matakan da kungiyar ke dauka, akwai na karbe wa duk wata burduwa wayar hannu, da hana su zuwa kasuwanni.

Wannan matakin ya zo ne a lokacin da daukacin matasa ke cin gajiyar yin amfani da wayar hannu masamman ma ta shafukan sada zumunci.

Ishaka Alhadji Manou shi ne shugaban kungiyar Bakandamiya reshen garin Touroua dake arewacin Kamaru. Ya ce sun dauki wannan mataki ne domin ladabatar da matasa masamman ma yara mata wadanda tarbiyyarsu ke tabarbarewa a yanzu haka sakamakon aron al'adun da suke wadanda sun zame baki ga bahaushe da kuma musulmi.

"Mun dauki matakai saboda yaranmu mun ga suna lalacewa, suna al'adu wadanda ba irin na Hausawa ne ba. Sai ka ga yarinya ta rike waya irin ta hannu guda uku ita kadai", in ji Isiaka Alhadji Manou.

Kungiyar ta koka da yadda matasa ke kwaikwayon al'adun da ba nasu ne ba, kuma ta sha alwashin canza lamarin.

A cikin matakan akwai hana dukkan budurwa ko bazawara zuwa kasuwannin kauye, da tabbatar da masu neman aure suna gabtar da kansu a gidan iyayen yarinya kafin a basu izinin ganawa da ita.

Shugaban kungiyar ta Bakandamiya ya kara da cewa, "Har ila yau, mai son yarinya da aure ya zo gidan ubanta."

Labarai masu alaka