Gobara ta raba Mutum 10,000 da muhallansu a Afirka ta Kudu

Knysna Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Gobarar ta lalata akalla wurare 150

Jami'ai a Afirka ta kudu sun ce mutum 10,000 ne suka tsere wa muhallansu saboda gobarar da ta mamaye wani gari dake kusa da teku, a kasar.

A kallah mutum takwas ne suka hallaka sakamakon gobarar, wacce ke kara yaduwa zuwa wasu yankuna a yammacin yankin Cape.

Iska mai karfi dake kadawa na kara rura wutar , da ba a taba ganin irinta ba cikin shekara 30.

Jami'an kashe gobara sun ce akalla wurare 150 ne suka lalace sakamakon gobarar.

Yawan jama'ar garin ya kai 77,000, kuma na yana murabba'in kilomita 500 daga gabashin birnin Cape Town.

Mai magana da yawun rundunar tsaron kasar ya ce jami'anta za su taimaka wajen zubo da ruwa ta sama a kokarinta na dakile gobarar.

Ya kara da cewa an kai jami'an tsaro 150, domin tabbatar da cewa barayi ba su sace dukiyoyin da aka kubutar ba.

Labarai masu alaka