FA ta ci tarar Moyes fam 30,000 saboda barazanar mari

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Moyes ya ajiye aikinsa bayan da Sunderland ta fadi daga Premier

Hukumara kwallon kafar Ingila FA ta ci tarar tsohon kocin Sunderland David Moyes tarar fam miliyan 30,000 saboda furtawa wakilyar BBC Vicki Sparks cewa "za ta sha mari" a watan Maris.

Moyes, ya yi wannan furuci ne, bayan da kungiyarsa ta Sunderland ta sha kaye a gida a hannun Burnley a gasar Premier.

Kocin dan Scotland, wanda ya ajiye aikin horar da kungiyar a watan Mayu bayan da ta fice daga gasar Premier, ya yi ta "bayyana nadama"ga kalaman nasa kan wakiliyar BBCn.

Hakan ya biyo bayan tambayar da Vicki ta yi masa kan cewa ko zuwan da Ellis Short ya yi, mai kulob din, ya kara sa shi cikin tsaka-mai-wuya?

Moyes ya amsa mata da a'a, amma kuma bayan sun kammala hirar tasu, sai ya ce da ita gara ta rika yi a hankali, ta bar ganin ita mace ce, don wataran za ta sha mari.

Tsohon kocin na Everton da Manchester United dai ya bai wa Misis Sparks hakuri daga baya, inda ya ce ya yi matukar da-na-sanin fadar wadannan kalaman.

Labarai masu alaka