Boko Haram: Bam ya kashe yara biyu a Adamawa

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption 'yan ta'adda sun bullo da sabon salo

Hukumomi a jihar Adamawa a arewa maso gabashin Najeriya sun ce wasu yara biyu sun rasa rayukansu, wasu uku kuma suka samu raunukka yayin fashewar wani abu da ake zato bom ne.

'Yan sanda a jihar sun ce lamarin ya faru da yammacin jiya Alhamis a kauyen Fadamar-Rake da ke yanki Hong, a lokacin da musulmi ke hidimar budin baki.

Bayanai sun nuna cewa wani mutum ne ya tsaya a wajen da yara ke wasa ya mika musu wani kunshi da ya ce kudi ne, ya ce su kai ma iyayensu, amma sai kunshin ya fashe.

A wata hira da ya yi da BBC kwamishinan watsa labaran jihar Ahmad Sajo ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya ce: "A gwamnatance mun tabbatar da cewa an jajanata wa iyayen yaran nan, marar lafiyar kuma an dauki dawainiyar ganin cewa sun samu lafiya, to amma mun kuma sa a yi bincike"

Ya kuma kara da cewa wannan kawai wani sabon salo ne da 'yan ta'adda suka bullo da shi don cutar da jama'a.

Labarai masu alaka