Ibrahimovic zai bar Man Utd

Zlatan Ibrahimovic Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Zlatan Ibrahimovic bai buga wa Utd wasa 10 a karshen kakar bana

Manchester united ta ki sabunta wa dan wasan gabanta Zlatan Ibrahimovic kwantiraginsa, bayan da kungiyar ta ki bayyana sunansa cikin 'yan wasan za ta rike har zuwa kakar wasa ta badi.

Hakan ya nuna cewa dan wasan dan kasar Sweden zai bar kungiyar a ranar 30 ga watan Yunin bana, lokacin da kwantiraginsa zai kare.

Ibrahimovic, mai shekara 35, ya kulla kwantiragin shekara daya da kungiyar a kakar da ta gabata, tare da zabin karin kakar wasa daya.

Sai dai sabunta kwantiragin dan wasan ya gamu da cikas, sakamakon ciwon gwiwa da ya yi fama da shi a watan Afrilu, inda hakan ya sa bai buga wasa 10 da kungiyar ta yi a karshen kakar ta bana ba.

Labarai masu alaka