Kotu ta yanke wa sojin Nigeria hukuncin kisa

Kotun ta ce ba za ta bari bara-gurbi su batawa soji suna ba Hakkin mallakar hoto Nigeria army
Image caption Kotun ta ce ba za ta bari bara-gurbi su batawa soji suna ba

Wata kotun sojin Najeriya da ke zaman ta a Maiduguri, babban birnin jihar Borno ta yanke wa wani soja hukuncin kisa saboda samun sa da laifin kashe wani mutum da ake zargi dan kungiyar Boko Haram ne.

Wata sanarwa da mataimakin daraktan hulda da jama'a na runduna ta bakwai ta sojin Najeriya, Kingsley Samuel ya fitar ta ce an samu Las kofur Hilary Joel da laifin "kisan mutumin da ake zargi dan kungiyar ta'adda ta Boko Haram a Damboa".

Sanarwar ta kara da cewa alkalin kotun Birgediya Janar Olusegun Adeniyi ya yanke hukunci ne a kan sojoji biyar bisa laifukan da suka shafi take hakkin dan adam da wasu manyan laifukan.

A cewar sanarwar, kotun ta kuma yanke hukuncin daurin shekara 15 kan Private Chima Samuel saboda samun sa da laifin taimakawa wurin kashe wani yaro Yakubu Isah a Maiduguri.

Kazalika mai shari'a Birgediya Janar Adeniyi ya rage wa Kofur Aliu Audu zuwa matakin Private saboda samun sa da laifin cin zarafi.

Haka kuma an rage mukamin Sajan Samuel Balanga zuwa matakin Private saboda samun sa da laifi biyu wadanda suka hada da gujewa daga bakin aiki da kuma wasu laifuka.

Kotun ta kuma yanke hukuncin daurin shekara biyu zuwa biyar kan Trooper Sunday Ogwuche saboda kama shi da laifin sata da kuma mallakar jigidar harsashi 641.

Alkalin kotun ya kara da cewa an yanke wadannan hukunce-hukunce ne domin raba rundunar soji daga bara-gurbi da kuma kare hakkin dan adama.

Ba wannan ne dai karon farko da ake yanke wa sojojin Najeriya hukunci kan keta hakkin dan adam ba.

Hakan na faruwa ne a yayin da kungiyoyin kare hakkin dan adam ke zargin rundunar sojin ta Najeriya da take hakkin dan adam a yakin da take yi da masu tayar da kayar baya, ko da yake sojoji sun sha musanta zargin.

Labarai masu alaka