Manyan muƙarraban Theresa May sun yi murabus

Nick Timothy da Fiona Hill Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Fiona Hill (daga hagu) da Nick Timothy

Wasu manyan muƙarraban Farai Ministar Birtaniya Theresa May biyu sun yi murabus bayan jam'iyyar Conservative ta kasa samun rinjayen da ake buƙata a babban zaben kasar.

An bukaci Misis May ta sallami Nick Timothy da kuma Fiona Hill ko kuma ta fuskanci kalubale wajen ci gaba da shugabancinta.

Mista Timothy ya ce ya dauki laifi dangane da rawar da ya taka wajen tsara manufofin jam'iyyar Conservative, wadanda 'yan majalisar dokokin kasar suke suka.

Misis May ta ce za ta ci gaba da kasancewa firai minista duk da rashin rinjayen da jam'iyyarta ta samu a babban zaben kasar da aka yi ranar Alhamis.

Jam'iyyar Conservative tana bukatar kujeru 326 ne gabanin ta kafa gwamnati, amma sai ta gaza samun hakan da kujeru takwas.

Birtaniya: Theresa May na fuskantar matsin lamba

Theresa May za ta nemi kafa sabuwar gwamnati

Ana saran firai ministar za ta bayyana sunayen ministocinta ranar Asabar, yayin da take kokarin kafa gwamnati ta hanyar kulla kawance da jam'iyyar DUP, wadda ta samu kujeru 10 a zaben.

Jam'iyyar Labour wadda ta zo ta biyu a zaben ta bukaci Misis May ta ba ta dama ta kafa gwamnati kuma ta soke ta kan batun hadakar da za ta kulla da jam'iyyar DUP.

Labarai masu alaka