U-20: Ingila ta ci Kofin duniya na matasa

Ingila Hakkin mallakar hoto Getty Images

Tawagar kwallon kafar Ingila ta lashe Kofin duniya na matasa 'yan kasa da shekara 20, bayan da ta doke ta Venezuela da ci 1-0 a ranar Lahadi.

Wannan ne karon farko da Ingila ta kai wasan karshe a wata babbar gasa ta duniya tun bayan lashe Kofin duniya da ta yi a shekara 51 da ta wuce.

Ingila ta ci kwallon ne tun kafin a tafi hutun rabin lokaci ta hannun dan Dominic Calvert-Lewin.

Sai dai kuma Venezuela ta kusa farke kwallon da aka zura mata, bayan da ta samu bugun fenariti, amma sai golan Ingila Freddie Woodman ya ture kwallon.

Labarai masu alaka