Ruwa ya lalata gadojin da ke haɗa Borno da Adamawa

Yankin da ruwa suka share gadoji
Image caption Taswirar Najeriya

Wani mamakon ruwan sama da ya shafe tsawon sa'o'i a yankin da ya raba jihohin Adamawa da Borno a Nijeriya ya yi sanadin ƙarasa karya wasu gadoji da ke haɗa jihohin yankin.

A cewar 'yar majalisar dattijai mai wakiltar Adamawa ta arewa, Sanata Binta Masi Garba gadojin Delchim da Kuzum na kan kogin Yesdarem na haɗa wasu jihohi a yankin na arewa maso gabashin ƙasar.

Ta ce ruwan sama ya yi awon gaba da gadojin ne a lokacin da mutanen yankin ke cin wata kasuwar mako-mako ranar Talata.

Sanata Binta Masi ta ce harkokin sufuri sun tsaya don kuwa a yanzu babu hanya.

Ta ce da ma gadojin suna cikin wani hali na rashin gyara, bayan sojojin Nijeriya sun tarwatsa su, sakamakon rikicin Boko Haram, da nufin hana 'yan ta-da-ƙayar-baya ci gaba da tsallakowa.

Ta ce gadojin su ne ke haɗa yankunan Gwoza da Askira Uba a cikin jihar Borno da kuma Michika da Madagali a jihar Adamawa kuma ta kansu mutanen jihohin Gombe da Yobe ke sufuri zuwa yankunan Taraba da sauran jihohi.

A cewarta an sanya kasafin kuɗin gyara gadodjin a cikin asusun kula da zaizayar ƙasa a baya, amma har yanzu gwamnati ba ta iya gyara su ba kafin ruwa ya sake lalata su.

Ta ce yankewar gadojin a halin yanzu ya hana dalibai zirga-zirga ba, haka ma ya hana marasa lafiya isa babban asibitin yankin da ke Michika.

Sanata Binta Masi Garba ta ce ta sha kai koke ga mahukunta don a gyara gadar amma abu ya ci tura.

Labarai masu alaka