Tsutsa na cinye shukar manoma a sassan Nigeria

Tsutsa mai cin anfanin gona Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Tsutsa mai cin anfanin gona

Wata tsutsa da ke mamaye gonaki ta fantsama kan shukar manoma musammam amfanin gona irinsu masara da gero da dawa da shinkafa a wasu sassa na Nijeriya.

Jami'ai sun ce matsalar ta fi ƙamari a jihohin Binuwai da Neja da Katsina da Oyo da kuma bayan-bayan nan Zamfara da Kano.

Sakataren ƙungiyar manoman shinkafa shiyyar arewa maso yammacin Nijeriya, Alhaji Sanusi Muhammad Gusau ya ce tsutsar ta yi mummunar ɓarna a gonaki musammam waɗanda shukarsu ba ta yi ƙwari ba.

A cewarsa tsutsar ta fi ɓarna a yankin tsakiyar Zamfara, ciki har da Gusau da Bunguɗu da Maru da Tsafe.

Ba ta damu da waken suya ko kuma tafasa ba ta fi cin shukar shinkafa da sauran amfanin hatsi.

Ya ce irin yawan tsutsar, zancen a ce za a yi feshi ma, ɓata lokaci ne kawai.

"Kai ba ka gan ta ba in tana hawan duwatsu baƙi ƙirin da ƙanananta da manya. Tana ci tana haihuwa, tana zubar da kashinta nan take."

Sakataren Manoman ya ce ana cikin mawuyacin hali saboda maganar feshin magani ma bai taso ba, kuma har yanzu ba su iya samun wani tallafin gwamnati ba.

Shi ma wani masani kan harkokin tsirrai a Oyo ya ce kashi 90 cikin 100 na gonakin masara da suka ziyarta a jihar, tsutsar ta addabe su ƙwarai da gaske.

Alhaji Sanusi Gusau ya ce tuni har wasu manoman da tsutsar ta cinye wa gonaki suka fara sake wata shukar, don kuwa a cewarsa tsoffin da suka san tsutsar sun ce idan ruwa ya sauka sosai za ta tafi.

Labarai masu alaka