Everton ta sayi Davy Klaassen a kan fam 23.6m

Klaassen Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Klaassen ya fara wasa a Ajax a shekarar 2011

Kulob ɗin Everton ya sayi kaftin din kulob din Ajax Davy Klaassen a kan fam miliyan 23 da dubu 600, inda ya kulla yarjejeniyar shekara biyar da shi.

Dan wasan tsakiyar tawagar kwallon kafa ta Holland, ya fara wasa ne a Ajax a shekarar 2011, inda zuwa yanzu ya yi wa wasa sau 163, ya zura kwallo a raga sau 49, ya kuma ci lig din gida sau uku.

Klaassen mai shekara 24 ya ce: "Ba na jin dadin barin Ajax, amma ina ganin yin hakan zai fi zame mini alheri," kamar yadda ya bayyana wa shafin inatanet na Everton.

Hakazalika, Everton ya sayi gola Jordan Pickford daga Sunderland a kan fam miliyan 25 - hakan ne karo na farko da za a sayi gola a kan wannan kudin a Birtaniya.

Klaassen ne ya yi wa Ajax kaftin a wasan da Manchester United ta doke su a wasan karshe na Gasar Europan bana.

Everton ta samu matsayi na bakwai ne a Gasar Firimiyar bana, wanda hakan yake nufin zai samu damar shiga Gasar Europa ke nan.

Labarai masu alaka