An umarci ’yan arewa su fice daga kudancin Nigeria

Igbo na a yankin kundancin Najeriya ne Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wasu al'ummar Igbo a Nigeria na neman kafa jamhuriyar Biafra

Wata gamayyar ƙungiyoyin tsagerun yankin Neja Delta mai arziƙin man fetur a Najeriya, ta nemi 'yan arewacin ƙasar da kamfanonin haƙar man fetur su bar yankinsu.

Ƙungiyoyin sun ba 'yan arewa da ke zaune a yankin wa'adin nan da ranar 1 ga watan Oktoba su fice daga yankin

Haka kuma, sun bukaci gwamnatin Nijeriya ta mayar musu da duk rijiyoyin man fetur da 'yan arewacin ƙasar suka mallaka a yankin.

Yayin da su kuma masu fafutukar kafa Biafra a yankin kudu maso gabashin ƙasar kuma suka umarci 'yan ƙabilar Igbo a kan lallai sai su bar yankin arewa su koma yankinsu na kudu maso gabashin Nijeriya.

Matakin dai ya biyo bayan wani wa'adin wata uku da wasu matasan arewacin Nijeriyar suka ba 'yan kabilar Igbo a kan su fice daga yankin arewaci.

Ga rahoton AbdusSalam Ibrahim Ahmed daga Enugu

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Wata gamayyar ƙungiyoyin tsagerun yankin Neja Delta mai arziƙin man fetur a Najeriya, ta n

Labarai masu alaka