'Ko APC da PDP sun taɓa taro kan matsalar 'yan ƙasa?'

APC Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Rashin ɗa'a a cikin tsarin jam'iyyu ciki har da APC da PDP ne silar taɓarɓrewar harkokin mulki a Nijeriya, in ji shugaban sabuwar jam'iyyar ADP

Shugaban wata sabuwar jam'iyyar siyasa a Nijeriya, Injiniya Yabagyi Yusuf Sani ya ce buƙatar tabbatar da ɗa'a a tsarin tafiyar da jam'iyyun ƙasar ce ta sanya su kafa jam'iyyar ADP.

Jam'iyyar ta Action Democratic Party (ADP) na ɗaya daga cikin jam'iyya biyar da hukumar zaɓen Nijeriya ta yi wa rijista a ranar Juma'a 16 ga watan Yuni.

Ya ce suna son dawo da tsari da ƙarfin da aka san jam'iyyun Nijeriya da su a jamhuriya ta ɗaya da ta biyu.

Injiniya Yabagyi ya ce rashin ɗa'a a tsarin jam'iyyu ne silar taɓarɓarewar harkokin mulki da na rayuwa a Nijeriya, ciki har da matsin tattalin arziƙi da ƙaruwar aikata laifuka da yunwa.

Daga cikin manufofin jam'iyyarsu ta ADP, a cewarsa akwai tanadin duk mutumin da ya ci zaɓe a ƙarƙashin inuwarta, to ita ce za ta tanƙwara shi, amma ba shi ya sanya ta a aljihu ba.

"Kai da aka tsai da kai, ka zama ko President (shugaban ƙasa) ko gwamna... Ka san cewa kai ɗan jam'iyya ne ba wai jam'iyyar nan...ta zama wadda za ka sa aljihu, ka yi abin da ka ga dama ba."

Ya ce jam'iyyar ADP za ta ba wa matasa da mata dama ta yadda su ma za a riƙa damawa da su.

"Shi ya sa muka sa a tsarin mulkin jam'iyyarmu cewa kashi 50 na waɗanda za su zama shugabanninta, su kasance matasa da mata."

A cewarsa, al'ummar Nijeriya sun gaji da abubuwan da ke faruwa na rashin haɗin kai da rikice-rikicen jam'iyyu.

Image caption Injiniya Yabagyi Sani ya ce duk da rikicin PDP gwamma ita da APC

Ya ce duk da rikicin shugabancin babbar jam'iyyar adawa ta PDP, rashin tsarin APC mai mulki ya fi lalacewa.

"Na PDP komai lalacewarsu, har gobe za su ce maka suna da....Kwamitin Amintattu, suna da Exco (shugabannin jam'iyya) suna meetings (taruka). Amma APC da ke mulki sun kasa kafa Kwamitin Amintattu, sun kasa convention (Babban taro na ƙasa). To party (jam'iyya) kenan?"

Ya ce bai kamata a ce sai lokacin da za a yi zaɓe sannan a waiwayi jam'iyya ko a ƙarfafa ta ba.

"Ba za ka taɓa jin... John Oyegun (shugaban jam'iyyar APC na ƙasa) ya gayyaci shugaban ƙasar Nijeriya ya zo....su yi taro a kan yadda za a tafiyar da al'amuran gwamnati ba."

"Ko kuma su tambayi shugaban ƙasa, a tambayi gwamnati cewa yaya kuke tafiyar da al'amuran gwamnati.

Ko me ya sa ake samun koma-baya ga arziƙin ƙasa da zaman lafiyar jama'a?."

"Kamar Oyegun, ya isa ya kira shugaban ƙasa, ko wani sakatare na gwamnati ko wani minista?" Injiniya Yabagyi ya tuhuma.

"ka taɓa jin kamar jam'iyyar APC ko PDP na taro na yadda za a gyara arziƙin ƙasa ko kuma a samu zaman lafiya?"

Ya ce idan ka ji (jam'iyyun) suna magana, batu ne kan riginginmunsu kawai, ba wai a kan jama'a ba. "Kuna bin manufarmu ko ba kwa bin manufarmu?"

A cewarsa bai shiga siyasa don yin kuɗi ba, don kuwa shi yana da aikin yi.

Ya ce: "Ire-irenmu nake kira su shiga siyasa, saboda a samu gyara."

Bai kamata a mayar da siyasa sana'ar mutanen da suka rasa aikin yi ba, ko kuma ta mutanen da ba su da gogewa a rayuwa ba, don kuwa duk matakin da suka zartar to, yana da tasiri a kan kowa da kowa, in ji shi.

Labarai masu alaka