Wane hali 'yan gudun hijira ke ciki?

Gwamna Shettima ya bukaci a ci gaba da hakuri Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Gwamna Shettima ya bukaci a ci gaba da hakuri

'Yan gudun hijirar da suka tsere daga gidajensu sakamakon rikicin Boko Haram sun ce rikicin ya zama wani kalubale da ba su taba fuskanta ba a rayuwarsu.

Sun bayyana haka ne a daidai lokacin da ake zagayowar ranar 'yan gudun hijira, wacce Majalisar Dinkin Duniya ta kebe domin tunawa da halin da miliyoyin 'yan gudun hijirar ke ciki da kuma bukatar tallafa musu.

Wata 'yar gudun hijira mai suna Kyallu ta shaida wa BBC cewa "sanadin rikicin Boko Haram babu wahalar da ba mu sha ba. Mun fice daga gidanmu ba tare da komai ba muka yi gudun hijira har zuwa Lagos kafin mu dawo Kaduna mu zauna."

A cewarta, rikicin na Boko Haram ya yi sanadin mutuwar danginta, ciki har da mahaifinta sannan mijinta ya tsere zuwa Lagos.

Wata 'yar gudun hijirar mai suna Fatima, wacce ta fito daga Maiduguri, ta gaya wa BBC cewa shekararta hudu tana gararamba tsakanin garuruwa daban-daban.

"Kananan sana'o'in da nake yi ne ya sa muke samun abinci amma gaskiya muna shan wuya", in ji ta.

Shi kuwa Mustapha Muhammad, wanda ya fito daga Bama, ya ce ya shafe shekara shida a Kaduna, yana mai cewa "kungiyar da muka hada ta 'yan gudun hijira ce ta sa muka samu sa'ida. Amma kafin wannan lokacin mun sha wahala sosai - babu abinci, babu tufafi, babu komai na more rayuwa".

Gwamna jihar Borno Kasshim Shattima ya gaya wa BBC cewa suna yin bakin kokarinsu wajen sake tsugunar da mutanen da rikicin Boko Haram ya kora daga garuruwansu musamma ganin cewa sojin Najeriya sun fatattaki 'yan Boko Haram din daga kusan daukacin garuruwan.

"Za mu taimakawa mutanen Mafa da Konduga da Dikwa za su koma garuruwansu. Amma a Bama babu wurin zama. Muna jira mu kammala gina gidaje da ofisoshin jami'an tsaro kafin mu gaya musu su koma. Don haka muna kira da su ci gaba da hakuri", in ji Gwamna Shettima.