Wata 'yar Nigeria ta yanke al'aurar wanda ya yi mata fyade

'Yan sanda a Najeriya Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Kotun ta fara sauraron karar ne a ranar Litinin da ya wuce

An gurfanar da wani mutum mai shekara 30 a gaban wata kotu, bayan yarinyar da ake zargin ya yi wa fyade ta yanki al'aurarsa, a jihar Katsina da ke arewa-maso-yammacin Najeriya.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sanda ta jihar, DSP Gambo Isa, ya shai da wa BBC cewa, asirin mutumin ya tonu ne bayan da ya je neman shaida a wajen 'yan sanda domin likitoci su duba raunin da yarinyar ta yi masa a al'aura.

Jami'in 'yan sanda ya kara da cewa an fahimci abin da ya faru ne bayan 'yan sanda sun yi masa tambayoyi, inda daga nan ne aka gane cewar ya ji ciwon ne a lokacin da yake yi wa wata yarinya fyade da karfin tuwo.

A halin yanzu dai mutumin da ake zargin na gidan wakafi, bayan alkalin kotun majistire, sai Mai Shari'a Fadile Dikko ya dage sauraren karar zuwa 20 ga watan Yulin mai kamawa.

Alkalin ya ce zai mayar da shari'ar ga rundunar 'yan sandan jihar Katsina da kuma daraktan gabatar da kara na jihar domin gurfanar da mutumin a gaban babbar kotu, saboda kotunsa bata da hurumin sauraron batun fyade.

Limamin coci ya yi wa yarinya fyade ta haihu

An tuhumi yarinyar da ta kashe 'wanda zai mata fyade'

An yanke hukuncin kisa ga wanda ya yi fyade

Bayanai daga jihar ta katsina na cewa lamarin ya faru ne a wani kango a karamar hukumar Kankara.

Lamarin dai ya faru ne a ranar 15 ga watan Mayun da ya wuce, amma ya fito fili ne a lokacin da shi mai fyaden ya je asibiti neman magani.

A karkashin doka a Najeriya dole ne mutum ya gabatar da bayanin amincewar 'yan sanda ga likitoci kafin su duba shi, idan rauninsa ya shafi wasu nau'uka ciki har da harbin bindiga.

Ga rahoton da Abdulwasiu Hassan ya hada mana:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Wata ta yanki mazakutar wanda ake zargin ya mata fyade

Kawo yanzu dai kotu ba ta tuhumi mutumin a hukumance ba kafin a ji ko zai amsa laifin ne ko kuma zai musanta shi.

Labarai masu alaka