Bankuna za su ƙwace iko da Etisalat

Bankunan na bin Etisalat bashin $1.72 bn Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Bankunan na bin Etisalat bashin $1.72 bn

Gamayyar wasu bankunan Najeriya ta ce za ta kwace ikon kamfanin Etisalat saboda ya gaza biyan bashin da suke bin sa.

Hakan na faruwa ne a daidai lokacin da rukunin kamfanin Etisalat da ke Hadaddiyar Daular Larabawa, ya janye hannun jarinsa - kashi 70 cikin 100 - daga Etisalat ta Najeriya.

Kamfanin sadarwa na Emerging Markets Telecommunication Services Limited, wanda ke rike da sauran kashi 30 na hannun jarin a Etisalat, ya gaza biyan bashin da bankunan ke bin sa.

Gamayyar bankunan, wadda bankin Access ke jagoranta, na bin Etisalat bashin $1.72 bn (kimanin N541.8 bn) wanda kamfanin ya ranta a 2015.

Batun kwace ikon Etisalat din dai ya janyo fargaba ga ma'aikatan kamfanin.

Sai dai a wata sanarwa da hukumar da ke sanya ido kan kamfanonin sadarwa, NCC, ta aike wa manema labarai, ta tabbatarwa masu mu'amala da Etisalat cewa su daina fargaba.

Sanarwar, wacce kakakin NCC Tony Ojobo ya sanya wa hannu, ta ce "hukumarmu tana tabbatarwa masu layin Etisalat 21m cewa za ta yi dukkan abin da ya dace bisa doka domin ganin sun ci gaba da more amfanin da layukan waya na Etisalat".

Mr Ojobo ya kara da cewa NCC tana daukar matakai masu muhimmanci wurin ganin ba a kwace iko da bankunan za su yi da Etisalat bai yi mummunan tasiri ba.

Labarai masu alaka