Ghana na binciken dan Nigeria mai satar mutane

Shugaban kasar Ghana Nana Akupo-Addo Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Yadda ake amfani da kafofin yada zumunta na ciwa hukumomin tsaron Afrika ta yamma tuwo a kwarya

Rundunar 'yan sandan Ghana ta ce ta fara bincike a kan wani dan Nigeria da ake zargin ya yi fice wajen satar mutane don neman kudin fansa.

Shugaban 'yan sandar kasar, David Asante-Apeatu ya ce za su yi musayar bayanai da takwaransa na Najeriya a kan Chikwudube Onwuamadike wanda hamshakin mai kudi ne.

Ya bayyana hakan ne a Accra a yayin wani taro kan tsaro a yankin yammacin Afrika da aka yi a birnin Accra a ranar Laraba.

Mista Apeatu ya nemi hadin kan sauran kasashen yankin a kan matsalolin tsaro da suka hada da ta'addanci da bazuwar kananan makamai da rashin aikin yi a tsakanin matasa da kuma rashin isassun kayan aiki ga hukumomin tsaro da ke yankin.

Shi ma babban sifeton 'yan sandan Nigeria, Ibrahim Idris yace bincikensu ya nuna cewa Chikwuduben yana da hannu a sace-sacen mutane da dama kuma yana karbar makudan kudaden fansa.

Inda ya kara da cewa mutumin da ake zargin yana da fasfo din Ghana da kuma na Najeriya.

Haka kuma hamshakin mai kudin da aka fi sani da suna Evans yana da gidaje biyu a Ghana, sannan iyalinsa na zaune ne a kasar ta Ghana.

An dai cafke mutumin ne a filin jirgin sama na Legas a ranar 10 ga watan Yuni, a yayin da yake shirin barin kasar.