Garuruwan da suka iya wargaza shirin Boko Haram

Boko Haram

Asalin hoton, Boko Haram

Bayanan hoto,

Binciken ya ce rashin haɗin kai na daga cikin dalilan da suka janyo ƙwace garin Gwoza da Boko Haram ta yi.

Wata ƙungiya mai taken Cibiyar bunƙasa fasahar sadarwa da ci gaban ƙasa (CITAD) ta wallafa wani bincike kan yadda wasu al'ummomi a Najeriya suka yi nasarar wargaza aniyar Boko Haram na mamaye musu yankuna.

Binciken wanda aka shafe tsawon shekara biyu ana gudanarwa, ya gano cewa sai bango ya tsage ƙadangare ke samun wurin shiga. Ya ce haɗin kai a tsakanin irin waɗannan al'ummomi ya zama babban makami na tunkarar ƙungiyar Boko Haram har ma da yin nasara a kanta.

Manufar binciken a cewar daraktan cibiyar, Yunusa Zakari Ya'u, ita ce kyautata haɗin kai tsakanin jama`a ta yadda za su guje wa faɗawa irin masifar da rikicin Boko Haram ya haddasa.

"Mun yi la'akari da cewa mutane ko kuma al'umma su ne ginshiƙin tsare kansu."

Ya zayyana ƙoƙarin al'ummomin garuruwa irinsu Biu da Gombi da Azare da unguwar Gwammaja a jihar Kano a matsayin abin misali ta fuskar wannan haɗin kai.

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

Garuruwa da dama a yankin arewa maso gabas sun kafa ƙungiyoyin matasa 'yan sintiri don kare yankunansu

Ya ce: "Idan ka ɗauki waɗannan wajaje, wajaje ne da ko dai sun hana 'yan Boko Haram su shigo su yi ɓarnarsu, ko kuma lokacin da suka shigo an fatattake su, an kore su."

A cewarsa sun kuma ga yankunan da ba su yi irin wannan jajircewa ba, lamarin da ya kai ga cin galaba a kansu.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

"In ka ɗauki su Mubi da Gwoza da Bama da Yadi Buni, waɗannan wajaje 'yan Boko Haram sun shiga, wasu wajajen har sarakunansu ma suka gudu ba ma mutanen ba."

Ya ce a duk lokacin da ka samu al'umma kanta ba haɗe yake ba, to ba za ta iya tunkarar masifa irinta Boko Haram ba.

Yunusa Ya'u ya ce a wasu wuraren, sun tarar cewa rashin haɗin kai tsakanin jami'an tsaro da al'umma ya haddasa ta'adi mafi muni daga ƙungiyar.

A cewarsa har yanzu, mutane ba su karɓi saƙon nan da ke cewa 'ɗan sanda abokin kowa' ba. Hakan ta sa lokacin da Boko Haram ta fara kai hari kan jami'an tsaro wasu mutane a wasu wurare har murna suke yi.

Ya ce hakan ya sage gwiwar jami'an tsaron ta yadda a lokacin da Boko Haram ta auka wa mutanen gari, su ma jami'an tsaro "suka riƙa noƙewa."

"Idan ka ɗauki Gwoza a jihar Borno, shi ne rabuwar kai kan bambancin addini wato tsakanin farko kowannensu yana ga idan Boko Haram ta auka wa wancan, ba shi akai wa ba, ba zai kawo gudunmawa ba. Daga baya dukkansu kuma wutar ta ci su."

Haka kuma "A Bama, bambancin tsakanin ɗariƙoƙi ne, in ji Yunusa Ya'u."

Don haka ya buƙaci gwamnati da al'umma su kyautata jajircewa don gudun kada masifa irinta Boko Haram ta zo ta shafe su.