An kashe soja guda a harin Kamaru

Wasu jami'an tsaro
Image caption Jami'an tsaron Kamaru sun jima suna fuskantar kalubalen tsaro a yankin arewa mai nisa

Rahotanni daga garin Balgaram a lardin arewa mai nisa da ke jamhuriyyar Kamaru sun nuna cewa wasu da ake zargin 'yan ta'adda ne sun kai hari kan barikin jami'an tsaro na Jandarmomi.

An kai harin ne da safiyar ranar Alhamis, inda maharan suka kashe soja guda da kuma wata yarinya matashiya mai shekaru 8 a duniya.

Haka kuma bayanai sun nuna cewa maharan sun kuma kwashi ganima a barikin.

Hakan na zuwa ne kwana daya bayan wani harin kunar bakin wake ya yi sanadin mutuwar fararen hula shida a garin Kolofata da ke yankin.

Yayin da 'yan kunar bakin waken su biyu suma suka rasa rayukansu a lokacin harin.

Yankin na arewa mai nisa a jamhuriyyar ta Kamaru ya hada iyaka da arewacin Najeriya, musamman ta jihohin Borno da Adamawa, inda kungiyar Boko Haram ke kai hare-hare.

Kawo yanzu dai babu wanda ya dauki alhakin kai harin, ko da yake a baya kungiyar Boko Haram ta sha kai hare-hare a yankin.

Labarai masu alaka