Ya matan da aka mutu aka bari ke rayuwa a Nigeria?

Boko Haram Crisis
Image caption Har yanzu akwai matan da rikicin Boko Haram ya raba da mazajensu na da yawa a sansanonin 'yan gudun hijira da ke Maiduguri

Wasu alƙaluma na Majalisar Ɗinkin Duniya sun nuna cewa matan da mazansu suka mutu a duniya, sun kai kimanin miliyan 245 kuma miliyan 115 a cikinsu suna fama da matsanancin talauci.

Nijeriya mai yawan jama'a kimanin miliyan 180 na da gagarumin kaso na irin waɗannan zawarawa.

Majalisar Duniya dai ta keɓe duk ranar 23 ga watan Yunin kowacce shekara, don tunawa da halin da matan da suka rasa mazajensu ciki da kuma bukatar tallafa musu.

A wasu lokuta, akan bar matan da mazansu suka mutu da ɗawainiyar 'ya'yan da aka bar musu.

Abin da ke sa wasunsu cikin mawuyacin hali da ƙasƙanci ciki har da yawon bara don tsira da rai.

Wata mace da BBC ta zanta da ita a wani masallaci cikin birnin Abuja, yayin karɓar sadakar abinci ta ce tun bayan rasuwar maigidanta wanda ya bar mata ɗa shida, abincin da za su ci ma yake gagara.

Ta ce daga jihar Katsina suka zo birnin tarayyar, don neman abin da za ta ciyar da kanta da 'ya'yanta.

"Shi ya sa yanzu ko, muka zo wurin karɓar abinci, saboda ba mu da abin da za mu ba yaran."

A cewar uwar marayun, yaran ba sa zuwa makaranta, don kuwa ba ta da halin ciyar da su ma balle a yi batun karatu.

Ta ce tana da burin 'ya'yanta duka su yi karatu, amma a cikinsu, ɗaya ce kawai ke zuwa makaranta.

"Ɗawainiya kam, sai dai Allah ke taya ni amma ni ke neman abin da za su ci su sha."

Nijeriya dai ƙasa ce mai tasowa, don haka ake samun iyalai ko gidaje masu yawan zuri'a.

Baya ga irin waɗannan mata da mazansu suka mutu suka bari a wasu yankunan Nijeriya, a yankin arewa maso gabas kuwa ɗumbin wasu ne rikicin Boko Haram ya mai da zawarawa.

Irin waɗannan mata da 'ya'yansu musammam a Maiduguri, na cikin halin tagayyara sakamakon raba su da mazan da suka dogara da su donn rayuwa.

Akasarin matan ba su da aikin yi, ko wata sana'a, lamarin da ke sa wasu yin bara don neman abin da za su ci.

A kwai ma wasu dubban irin wadannan mata da 'yan tada-ƙayar-baya suka kashe mazajensu da ke samun mafaka a gidajen 'yan'uwa da abokan arziki, wasu kuma a gidajensu na gado.