Muna neman haƙuri da ƙarin goyon baya - Buratai

Buratai Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Janar Buratai ya ce suna neman goyon bayan jama'a kan ƙoƙarinsu na ci gaba da samun nasara a kan Boko Haram

Babban hafsan sojin ƙasa na Nijeriya, Laftanal Janar Yusuf Tukur Buratai ya ƙalubalanci dakarun da ke yaƙi da Boko Haram da cewa su ne da alhakin raba ƙasar da ayyukan ta'addanci.

Da yake jawabi yayin wata hira da BBC, Janar Buratai ya ce ya sha bayani game da batun sassauya sojojin da ke fagen daga wajen yaƙi da 'yan ta-da-ƙayar-baya idan sun shafe wani lokaci a can.

A cewarsa, wani soja ya taɓa tambayarsa a kan batun karon farko da ya kai ziyara arewa maso gabas, cewa sun yi shekara biyu zuwa uku a yankin.

Buratai ya ce amsar da ya ba shi ita ce: "wannan ƙasar, ƙasarmu ce. Ina ne za a canza ka, ka je? Da a ce muna ƙasar waje ne, an san cewa bai kamata ka jima fiye da kima ba."

"Amma wannan ƙasarka ce, dole mu zauna mu kare ta."

Babban hafsan ya ce yakan umarci kwamandojinsa a kan su riƙa ba wa sojojinsu hutun da suka cancanci samu.

"Ina gaya wa kwamandojinsu, su dinga ba su hutu suna tafiya," in ji shi. "Ya kamata kowa ya riƙa zuwa hutu, sai dai idan wani ya ce an hana shi hutu, to su yi mana bayani, za mu san matakan da za mu ɗauka."

A cewar Buratai, hare-haren ƙunar-baƙin-wake da ake ci gaba da fuskanta a yankin arewa maso gabas, abu ne da ke buƙatar ƙarin haƙuri.

"An samu nasara, insha Allahu, kuma wannan nasara ta riga ta tabbata. Insha Allahu za mu samu ƙarin nasara a gaba."

Ya ce yana neman ƙarin goyon baya da haƙuri daga wajen jama'a, da nufin daƙile Boko Haram da waɗanda "'yan koren" da ke ba wa ƙungiyar bayanai a cikin jama'a.

Janar Buratai ya ce babu tabbas kan iƙirarin da wasu ke yi cewa mai yiwuwa musayar da aka yi da 'yan matan Chibok ta hanyar sakin wasu kwamandojin Boko Haram ta sake ƙara wa ƙungiyar ƙaimin kai hare-hare.

Labarai masu alaka