Saudi Arabia ta kara wa 'yan ci-rani wa'adin ficewa daga kasar

Wasu 'yan ci-rani 'yan Habasha a Saudi Arabia Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Saudiyya ta ba wa 'yan ci-rani marasa takardun zama a Saudiyya karin lokacin ficewa daga kasar

Saudiyya ta kara tsawon wa'adin kwana 90 ga 'yan ci-rani marasa takardun zama a kasar, in ji jaridar Fana mai alaka da gwamnatin Habasha.

A ranar Talatar data gabata ne ya kamata shirin afuwar ya kare, amma akwai dubban 'yan Habasha da har yanzu suke makale a kasar saboda lokaci ya kure musu, in ji gwamnatin ta Habasha.

Ministan Sadarwa, Negeri Lencho, ya fada wa BBC cewa gwamnatin kasar ta nemi Saudiyyar ta kara wa 'yan kasar lokaci domin su fice daga kasar.

A baya dai Saudiyyar ta bukatar 'yan ci-ranin marasa takardun zama su fice kafin karshen watan Maris din da ya wuce.

Saudiyya ta yi wa marasa izinin takardun zama afuwa daukar mataki a kansu, amma ta bukaci su fice daga kasar.

Amma jaridar Arab News ta intanet ta ba da rahoton cewa an kara tsawon shirin afuwar da kwana 30 ne kawai.