Amurka ta jinkirta ɗaukar mata-maza aikin soja

James Mattis Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mista Mattis ya ce akwai buƙatar ƙarin lokaci don tsai da shawara a kan batun

Sakataren Tsaron Amurka James Mattis ya amince da jinkirta wani shirin gwamnatin Obama na ɗaukar mata-maza aiki a rundunar sojin ƙasar da tsawon wata shida.

Sabuwar manufar, wadda za ta ba wa dakarun Amurka damar sauya jinsi a lokacin da suke aiki tare da tsaida mizani na ayyukan kula da lafiya, a yanzu za ta fara aiki daga ranar 1 ga watan Janairun 2018.

Jami'an ma'aikatar Pentagon sun ce rundunonin sojin Amurka ba su cim ma yarjejeniya ba kan lokacin da za su fara karɓar sabbin sojojin.

Masu fafutukar kare 'yanci sun ce an ba su kunya da wannan jinkiri.

Wata sanarwa da wani mai magana da Gangamin tabbatar da 'yancin Ɗan'adam, Stephen Peters ya fitar ta ce:"Duk da ranar da ta wuce ba tare da fara aiki da wannan manufa ba, an samun tarnaƙi a rundunar sojojin Amurka na ɗaukar haziƙai da mutanen da suka yi fice aiki ba tare da la'akari da jinsinsu ba."

The secret life of a transgender airman

Jaridar Washington Post ta ambato Mista Mattis na cewa akwai buƙatar ƙrin lokaci don zartar da shawara a kan batun bayan tuntuɓar manyan jami'an tsaro, ya ƙara da cewa jinkirin "ta kowacce hanya ba ya nuna an gama tsaida magana".

Mai magana da yawun ma'aikatar Pentagon Dana White ta faɗa a cikin wata sanarwa cewa an samun jinkirin ne don hukumomin soja su iya yin bita game da tsare-tsarensu na karɓar aiki da kuma bayar tasu gudunmawa kan tasirin zama cikin shiri da zafin hannun dakarunmu."

Wani nazari da rundunar sojin Amurka ta ƙaddamar ya ƙiyasta cewa akwai jami'an soja tsakanin 2,500 zuwa 7,000 mata-maza a cikin illahirin dakarunta miliyan ɗaya da dubu 300, da kuma ƙarin 1,500 zuwa 4,000 a tsakanin rundunoninta na wucin gadi.

Labarai masu alaka