'Yan sanda sun kashe 'yan bindiga 19 a Mexico

Mexico Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan bindigan sun kashe wasu mutane uku ne, sannan kwatsam, 'yan sanda dake kusa suka musu dirar miliya

'Yan sanda a Mexico sun ce sun kashe 'yan bindiga goma sha tara, a musayar wuta da suka yi da su a jihar Sinaloa dake arewacin kasar.

Jami'an 'yan sanda biyar sun samu raunuka a bata kashin.

A daren Juma'a ne a ka fara bata kashin a garin Villa Union, lamarin kuma ya lafa bayan 'yan sanda sun yi ta tsere da 'yan bindigar a mota a Aguaje.

Jami'ai sun ce wannan, ya na daya daga cikin arangama mafi muni da aka yi a kudancin Sinaloa a 'yan watannin nan.

Yankin ya yi fama da rikice-rikice na wata babbar kungiyar masu hada-hadar miyagun kwayoyi a Sinaloa tun bayan da aka kama shugabanta a bara.

Wani rahoto ya ce 'yan bindigan sun kashe wasu mutane uku ne, sannan kwatsam, 'yan sanda dake kusa suka musu dirar miliya.