Ko Nigeria ka iya yin wani tasiri a rundunar Sahel?

Mali's militants

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

'Yan ta-da-ƙayar-baya masu iƙirarin jihadi a arewacin Mali sun addabi ƙasashen yankin Sahel inda suke kai hare-hare kan iyakokinsu

Wasu masharhanta harkokin tsaro sun ce rashin shigar manyan ƙasashe masu faɗa-a-ji kamar Najeriya da Algeria da Amurka, ka iya zama ƙalubale ga rundunar ƙasashen yankin Sahel biyar da za a kafa.

A ranar Lahadin ne shugabannin Mauritania da Nijar da Burkina Faso da Chadi da kuma Mali ke fatan daddale goyon bayan ƙasashen yamma ga rundunar mai soja dubu biyar da za ta fara yaƙi da 'yan ta-da-ƙayar-baya masu iƙirarin jihadi a yankin Sahel.

Wani mai sharhi, Malam Kabir Adamu ya ce daga cikin ƙalubalan da rundunar za ta iya fuskanta akwai batun ƙarancin kuɗaɗen gudanar da ita da horo kan yaƙi da ta'addanci da kuma samar da kayan aiki ga rundunar.

"Duka ƙasashen guda biyar da ke ciki, suna da matsalar ta'addanci. Mu kanmu nan ƙasa Najeriya, akwai hasashen da ke nuna cewa matsalolin da ke tasowa daga can suna shafarmu," in ji shi.

Bayanan hoto,

Karo na biyu kenan da Mista Emmanual Macron zai ziyarci Mali tun bayan hawan mulkin Faransa

Shugaban Faransa, Emmanuel Macron na halartar taron ƙoli, kuma "ana sa ran bayanan sirri da ƙasarsa ke tattarawa, wata muhimmiyar gudunmawa ce ga rundunar ta ƙasashen Sahel" a cewar Kabir.

Taron dai na zuwa ne bayan dubban mutane sun gudanar da wata zanga-zanga a Bamako babban birnin Mali ranar Asabar don nuna rashin jin daɗinsu ga ƙudurin yi wa tsarin mulkin ƙasar gyaran fuska.

Shugaba Ibrahim Boubacar Keita ya buƙaci a gudanar da ƙuri'ar raba gardama a kan tsare-tsaren kafa majalisar dattijai a ƙasar.

Batun da 'yan adawa suka yi watsi da shi, inda suka ce gyare-gyaren da aka ƙuduri aniyar yi magoya bayansa za su fifita ta hanyar ba su iko mai yawa a majalisa.

Suka ce tunkarar 'yan ta-da-ƙayar-baya masu iƙirarin jihadi a yankunan tsakiya da arewacin Mali, ya fi a'ala yanzu a kan shirya ƙuri'ar raba gardama.

Faransa ta tura dubban dakaru ƙasar don kakkaɓe 'yan ta-da-ƙayar-baya masu alaƙa da al-Qaeda a arewacin ƙasar.

Wakiliyar BBC ta yi hasashen cewa mai yiwuwa Mista Macron zai so aza harsashin wani tsari na janye dakarun ƙasarsa a nan gaba, waɗanda kasancewarsu tare da dakarun kiyaye zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya dubu 10 a Mali, bai tsamo ƙasar daga cikin halin rashin tabbas ta fuskar tsaro ba.