Jamus ta dauki Kofin Zakarun Nahiyoyi bayan ta doke Chile 1-0

Lars Stindl kenan a lokacin da ya zura kwallo a ragar Chile da Claudio Bravo ke tsaro Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Lars Stindl a lokacin da ya zura kwallo a ragar Chile da Claudio Bravo ke tsaro

Zakarun duniya 'yan Jamus sun dauki kofinsu na zakarun nahiyoyi na farko bayan sun doke Chile 1-0 a wasan karshe da suka yi a daren Lahadin nan a Rasha.

Lars Stindl ne ya ci wa Jamus kwallon minti 20 da fara taka leda bayan wani mummunan kuskure da dan bayan Chile Marcelo Diaz ya yi.

A kusan karshen wasan da aka yi a birnin St Petersburg, 'yan wasan Chile Arturo Vidal da Angelo Sagal sun barar da damar farkewa.

Da wannan nasara yanzu cikin shekara uku Jamus ta dauki Kofin Duniya da na Zakarun Nahiyoyi da kuma kofin kasashen Turai na 'yan kasa da shekara 21.

Tun da farko Portugal ta doke Mexico da ci 2-1 ta sami matsayi na uku a gasar.

Gasar ta zakarun nahiyoyi tana zaman kamar shiri ne na tunkarar gasar cin kofin duniya, inda ake yinta a kasar da za a yi ta kofin na duniya shekara daya kafin ta kofin na duniya.

Kasashe takwas ne suke shiga gasar, wadanda suka hada da shida da suka dauki kofin nahiyoyinsu da kasar da ta dauki kofin duniya da kuma mai masaukin baki.