Syria: Ana gab da karbe birnin Raqqa daga hannun IS

Sojojin Syria a bakin aiki
Image caption IS ta lalata kusan dukkan manyan wurare da ke birnin Raqqa

Dakarun kawancen da Amurka ke jagoranta a kasar Syria sun ce gamayyar kungiyoyin 'yan tawayen Syrian Democratic Forces sun tsallaka katangar tsohon birin Raqqa.

Inda ka yi amanna da cewa nan mayakan kungiyar IS ke da rinjaye.

Sun kara da cewa sun taimaka musu ta hanyan yin luguden wuta a bangare biyu na katangar, ta inda sukai barin wuta ta ko ina.

Wannan ya bai wa dakarun shiga birnin ta ko'ina, hakan kuma ya ba su damar hana mayakan IS tada abubuwan fashewa da suka binne a wasu wurare a birnin na Raqqa.

Yaki da gwagwarmayar karbo birnin Raqqa daga hannun 'yan IS na zuwa ne, a daidai lokacin da suma sojojin Iraqi ke cewa sun fara yin galaba akan masu ikirarin kafa daular musulunci da suka addabi kasar, dakarun soji da na kawance sun ce su na gab da karbe baki dayan arewacin birnin Mosul wanda shi ne babbar maboyar IS.

Labarai masu alaka