Sake harba makamin Koriya ta Arewa 'tsokanar fada ne'

Makamin Koriya ta Arewa mai cin dogon zango
Image caption Shugaba Shinzo Abe na Japan ya ce gwajin makamin Arewa na tsokanar fada ne

Koriya ta Arewa ta sake harba wani makami mai linzamain da sojojin Amurka suka ce ya yi tafiyar minti 40 kafin ya fadi a tekun kasar Japan.

Wakilin BBC a birnin Seoul ya rawaito cewa tsahon lokacin da makamin ya dauka kafin ya fadi ya nuna yadda Arewa ta kara karfin makami mai linzamin ta idan aka kwatanta da gwaje-gwajen baya da ta yi.

Wannan gwajin dai ya sha banban da na baya, saboda tsahon lokacin da ya dauka, kwatan-kwacin tafiya a jirgin sama ne zuwa wa jiha da ke birnin.

A watan Junairu shugaba Trump ya sha alwashin ba za a bar Arewa ta samar da makami mai linzami mai cin dogon zangon da zai kai har Amurka ba.

Shugaba Shinzo Abe na Japan ya zargi Arewa da yin watsi da gargadin da aka sha yi ma ta kan gwajin makami, ya yi kira ga aminanta China da Rasha su kara matsa lamba dan kar a sake hakan.

A bangare guda kuma shugaba Donald Trump a wani sakon tweeter da ya wallafa, ya yi kira ga China ta karo karshen abinda ya kira aikin banzan da Arewa ke yi baki daya.

Labarai masu alaka